Ba a saida Asibitin Hasiya Bayero ba – Tsohon Kwamishinan Kano

Daga BASHIR ISAH

Tsohuwar Gwamnatin Jihar Kano ta ce karkatar da hankalin ‘yan jihar ne iƙirarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kan cewa an sayar da asibitin yara, wato Hasiya Bayero, da ke birnin jihar.

Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya faɗa a ranar Litinin cewar an dakatar da harkoki a asibitin ne na wucin-gadi biyo bayan sake masa matsuguni bayan kammala asibitin yara na Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu, ɗaya daga cikin ayyukan da Gwamnatin Ganduje ta gada.

Ya ƙara da cewa, asibitin wanda aka faɗaɗa tare da inganta shi fiye da da zai kuma kasance cibiyar ba da horo da kuma bincike.

Ya ce an buƙaci a maida tsohon matsugunin asibitin na Hasiya Bayero ya zama cibiyar kula da matsalolin da akan yi fama da su sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Ƙari a kan haka, tsohon Kwamishin ya ce tsohuwar gwamnatin jihar na da niyar ƙirƙiro masarrafar abinci mai gina jiki a wajen don yaƙi da matsalar rashin abinci mai gina jiki da sauransu.

Ya ce a wancan lokaci har Gwamnatin Ganduje ta kafa kwamitin da zai lura da yadda aikin cibiyar zai gudana.

Wanda har kwamitin ya samu kai ziyara ƙasar Nijar domin binciken da zai taimaka wajen samar da ingantacciyar cibiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *