Gwamnan Kano ya ƙwace asibitin Hasiya Bayero da Gwamnatin Ganduje ta sayar

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya ƙwace fitaccen asibitin yara ɗaya tilo da ke cikin birnin Kano wanda aka fi sani da Hasiya Bayero.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai asibitin a ranar Lahadi inda ya duba halin da asibitin ya ke ciki.

Asibitin na Hasiya Bayero dai ya shafe shekaru 33 yana aiki, wanda ya shahara wajen karɓar yara marasa lafiya daga ilahirin ƙananan hukumomin jihar da kuma maƙwabtan jihohi.

Engr Abba ya bayar da umarnin a gyara asibitin nan take, a mayar da shi na zamani domin al’umma su ci gaba da cin moriyarsa.

Gwamnan ya nuna ɓacin ransa yadda ana tsaka da amfani da asibitin, amma gwamnatin Ganduje ta siyar da shi ta kuma tashi jama’a marasa lafiya da likitoci.

“Kowa aka ba asibitin Hasiya Bayero mun ƙwace shi, kuma mun dawo wa da talakawa haƙƙinsu,” in ji Gwamnan.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin tsohon gwamna Ganduje ce ta siyar da asibitin a kan Naira miliyan 6.