Kotu ta haramta karuwanci a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Alƙali James Kolawole Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba, ya yi watsi da ƙarar da ke neman masu sana’ar karuwanci a Babban Birnin Tarayya Abuja su ci gaba sa sana’arsu ba tare da tsoratarwa daga hukumomin tsaro ba.

A hukuncin da ya yanke, alƙalin ya ce, karuwai ba su da wani haƙƙi na doka da za su ci moriyar wata doka da aka sani ko kuma Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya.

Mai Shari’a Omotosho ya ci gaba da cewa, saboda haka za a iya tuhuma da kama masu yin lalata da kuma karuwan, a gurfanar da su a gaban kuliya, don fuskantar ɗaurin shekaru biyu a gidan yari a ƙarƙashin dokar hana aikata manyan laifuka da aka fi sani da ‘Penal Code’.

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Lawyers Alert Initiatiɓe for the Protection of Rights of Children, Women and Initiatiɓe, ta maka hukumar kare muhalli ta Abuja, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) a matsayin waɗanda ake ƙara na 1 zuwa na 4 a shari’ar.

A cikin ƙarar mai lamba THC/ABJ/CS/642/2024, karuwan sun nemi hana ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da AEPB cin zarafi, tsoratarwa, kamawa da gurfanar da su a Abuja.

Sun buƙaci alƙalin da ya aiwatar da muhimman haƙƙoƙinsu na ɗan Adam na karuwanci kamar yadda dokar Nijeriya ta tanada.

ƙararrakin da aka shigar a ranar 14 ga Mayu, 2024, ta hannun wata tawagar lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Rommy Mom, Bamidele Jacobs da ɓictor Eboh, sun tada tambayoyi biyu domin yanke hukunci daga alƙali.

Ta roƙi kotun da ta tantance ko aikin AEPB a ƙarƙashin sashe na 6 na dokar AEPB na shekarar 1997 ya shafi cin zarafi, kamawa, tsarewa da gurfanar da matan da ake zargi da yin lalata a titunan Abuja.

Ko a tanadin Sashe na 35 (1) (d) na Dokar AEPB, 1997, ana iya ɗaukar mata a matsayin kasidu ko jikinsu a matsayin kayan saye.

Lauyoyin sun nemi a bayyana cewa tuhumar da ma’aikatan AEPB suka yi a gaban kotun tafi da gidanka ta FCT, wanda ya ce an kama matan da ake zargi da sana’ar karuwanci a matsayin ‘labarai’ tare da ɗaukar jikinsu a matsayin ‘kayan da za a saya,’ na nuna wariya ne kuma ya saɓa wa tanadin sashe na 42 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

Sun nemi a bayyana cewa aikin hukumar bai shafi cin zarafi, kamawa da kuma kai samame ga mata da ake zargi da yin lalata a titunan Abuja ba.

Sun kuma nemi a bayyana cewa ba sashe na 6 na dokar AEPB na shekarar 1997, ko wasu wasu dokokin ƙasar da suka ba hukumar damar cafke mata da ake zargi da yin lalata a titunan Abuja.

Sun kuma nemi a ba da sanarwar cewa sashe na 35 (1) (d) na dokar AEPB, 1997, ba ya kiran mata a matsayin ‘kasidu’ ko kuma a ɗauki jikinsu a matsayin ‘kayan saye.

Don haka lauyoyin sun roƙi kotun da ta ba su umarnin hana hukumar AEPB, jami’anta ko masu zaman kansu cin zarafi, kamawa da kuma kai farmaki ga matan da ake zargi da aikata lalata a titunan Abuja.

Sai dai alƙali a cikin hukuncin da ya yanke ya ce ko da ya cancanta, “aikin da ake nema bai dace ba, don haka an kori ƙarar saboda rashin cancanta.