
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Babbar Jam’iyyar adawa (PDP) da ta dakatar da babban taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa a ranakun Asabar da Lahadi a Ibadan, Jihar Oyo.
Kotun, a shari’ar da Alƙali Peter Lifu ya yi hukunci, ya kuma haramta wa Hukumar Zaɓe (INEC), sanya ido ko amince wa sakamakon taron matuƙar aka gudanar da shi ba tare da amincewa da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo a matsayin ɗaya daga cikin ƴan takarar shugabancin jam’iyyar ba.
A cewar kotun, hujjar da aka gabatar mata ta nuna cewa an hana Lamiɗo damar tsayawa takarar ne ba bisa doka ba, wanda hakan ya saɓa wa dokar ƙasa da ta jam’iyyar.
A wata takarda da mai taimaka wa tsohon gwamnan akan yaɗa labarai, Mansur Ahmed Hassan ya fitar, ya ce kotun ta wajabta wa jagorancin jam’iyyar bai wa mambobinta damar tsayawa takara ta hanyar gindaya musu sharuɗɗa domin su samu cimma manufofinsu.
Kasancewar jam’iyyar ta gaza bin umarnin kundin dokokinta ya sa mai shari’ar ya umarci a dakatar da taron har sai an ba Lamiɗo damar mallakar fom ɗin tsayawa takara da yaƙin neman zaɓe.
