Matsalar tsaro: Gwamnatin Dauda Lawan ta ƙi ba gwamnatin tarayya haɗin kai – Matawalle

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ƙaramin Ministan Tsaro, Hon. Bello Matawalle ya bayyana cewar, gwamnatin tarayya ta tura ƙarin sojoji zuwa jihar Zamfara domin yaƙi da ‘yan ta’adda.

Ministan ya yi wannan sanarwar ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a sakatariyar jam’iyyar dake Gusau babban birnin Jihar Zamfara a yau Juma’a.

A cewarsa, matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka ya zama dole idan aka yi la’akari da cewa Zamfara na fuskantar rashin tsaro sakamakon sake ɓullar hare haren ‘yan ta’adda.

Matawalle ya tabbatar wa mutanen Zamfara cewa, gwamnatin tarayya tana yin duk mai yiwuwa don tabbatar da zaman lafiya ya dawo jihar.

A cewar sa, tuni sojojin sun riga sun iso jihar, yana mai cewa an ba su umarni mai ƙarfi don tabbatar da su yaƙi ƙungiyoyin ‘yan bindiga da suka addabi al’ummar jihar a duk inda suke ɓoye a jihar.

Matawalle ya kuma yi Allah wadai da rashin goyon bayan gwamnatin tarayya daga gwamnatin Gwamna Dauda Lawal kan matsalar rashin tsaro da ke shafar jihar, yana mai cewar, matsalar rashin bai wa gwamnatin tarayya haɗin kai daga gwamnatin jihar ya gurgunta ƙoƙarin gwamnatin tarayya a yaƙi da ‘yan bindiga a jihar.

“Na yi duk abin da zan iya don yin aiki tare da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal kan rashin tsaro da ke shafar jihar Zamfara, amma yaƙi bamu goyon bayan da ya dace”. Matawalle ya ce.

Ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan shimfiɗa tagwayen hanya daga Zaria-Funtua-Gusau zuwa Sokoto.

A cewarsa, aikin zai bunƙasa tattalin arzikin jihohi huɗu na Kaduna, Katsina, Zamfara da Sokoto tare da sauƙaƙa hanyoyin sufuri.

Matawalle ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayan ta, da su ci gaba da kasancewa ‘yan ƙasa nagari masu haɗin kai da bin doka domin nasarar jam’iyyar a shekarar 2027 a ƙasar.

By ukarofi