‘Yan bindigar da suka yi awon-gaba da daraktocin Ma’aikatar Tsaro shida sun nemi a biya miliyan N150

Spread the love

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaro sun nemi kuɗin fansa har N150 miliyan, lamarin da ya ƙara gigita iyalan mutanen da aka sace, tare da jefa su cikin damuwa kan yadda za su iya tattara irin wannan maƙudan kuɗaɗen.

Iyalan waɗanda abin ya faru da su sun bayyana cewa buƙatar kudin ta ƙara tsananta musu raɗaɗin mikin ciwon da suke fama da shi.

“Har yanzu muna cikin fargabar abin da ya faru. Yanzu kuma suna neman Naira miliyan 150 domin sakin su shida gaba daya. Ta yaya za mu iya hada wannan kudin? Muna rokon su da su saki ’yan’uwanmu ba tare da wani lahani ba”, kamar yadda wani daga cikin iyalan ya bayyana.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daraktocin, wato Mrs Ngozi Ibeziakor, Mrs C. Emeribe, Mrs Helen Ezeakor, Mrs C. Ladoye, Mrs J. Onwuzurike, da Mrs Catherine Essien — an sace su ne ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, a kan titin Kabba zuwa Lokoja yayin da suke tafiya daga Legas zuwa Abuja domin rubuta jarabawar karin girma ta matakin Darakta.

Kungiyar Ma’aikatan Gwamnati ta Nijeriya, ASCSN, ta yi alla-wadai da lamarin a cikin wata sanarwa da Shugabanta, Shehu Mohammed, da Sakataren Janar, Joshua Apebo, suka sa hannu, inda suka ce daraktocin mambobin ƙungiyarsu ne, kuma ma’aikatan Command Day Secondary School, Ojo, Legas ne.

Kungiyar ta ƙara da cewa Ma’aikatar Tsaro ta tura jami’an tsaro domin neman hanyoyin ceto su, tare da sake kira ga gwamnatin tarayya da ta daina tilasta ma’aikata yin doguwar tafiya zuwa Abuja don jarabawar karin girma.

Hukumomin tsaro sun bayyana harin a matsayin “shiri na musamman da aka tsara tsaf,” abin da ya kara tayar da hankalin jama’a kan matsalar tsaro da barazanar da ma’aikatan gwamnati ke fuskanta a hanyoyi.

A halin yanzu, iyalan wadanda aka sace na ci gaba da rokon ’yan bindigar da su nuna tausayawa, su saki mahaliccinsu cikin koshin lafiya.

By Babaji