
An samu saɓani tsakanin dakarun sojoji da wasu jami’an ƴan sanda a jihar Benuwai da ke yankin Arewa ta Tsakiyan Nijeriya, lamarin da ya haddasa harbe-harbe da kaiwa ga jikkata mutum ɗaya.
Al’amarin ya auku ne bayan sojoji sun yi yunƙurin tsayar da ƴan sanda a wani shingen binciken da suka sanya a kan hanya.
Rikicin ya auku ne a garin Naka da ke yankin Ƙaramar Hukumar Gwer ta Yamma a
ranar Talatar da ta gabata.
Wannan al’amari ya jefa al’umma cikin tashin hankali a garin wanda yawancin mutanen da ke cikinsa ‘yan gudun hijira ne.
An kuma gano cewa motar ofishin kwamandan rundunar JTF, CSP Lyam Akegh, ta lalace sakamakon harbin bindiga a yayin arangamar.
Shaidu sun ce an samu hatsaniyar ne a lokacin da jami’an JTF suke dawowa daga aikin sintiri da ya shafi yaƙi da ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a kan titunan Makurdi zuwa Ankpa da Naka zuwa Agagbe, lokacin da sojojin da ke shingen bincike a yankin suka tsayar da su.
A nasa bangaren, mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Benue kan tsaro da harkokin cikin gida, Joseph Har, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba don haka ya ƙaurace wa bada ba’asi a kai.
