
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Biyo bayan yadda ɗan wasan gaba na Super Eagles, Alex Iwobi ya zama na huɗu a jerin ƴan wasan da suka fi buga wasanni mafi yawa a tarihin tawagar ƴan ƙwallon Nijeriyar, Blueprint Manhaja ta zayyano ‘yan wasa guda 10 mafi yawan taka wa Nijeriya leda.
Iwobi, wanda ke buga wa ƙungiyar Fulham ta ƙasar Ingila, ya wakilci Super Eagles a jimillar wasanni 90, lamarin da ya ba shi damar yin kankankan da tsohon tauraron ɗan wasa, wato John Obi Mikel.
Ga jerin ƴan wasan da suka fi yawan wasanni a Super Eagles tun daga na ɗaya:
Ahmed Musa – 111
Vincent Enyeama – 101
Joseph Yobo – 100
Alex Iwobi – 90
John Obi Mikel – 90
Moses Simon – 86
Nwankwo Kanu – 86
Muda Lawal – 86
A halin yanzu Iwobi yana da shekaru 28 a duniya, wanda ake ganin ya ɗauko hanyar kafa tarihi na zama wanda ya fi kowane ɗan wasa yawan wasanni a tarihin Super Eagles.
