Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Jihar Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ofemai Ofem, ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar tana ƙalubalantar nasarar Gwamna Nasir Idris.
Da yake yanke hukuncin a gaban lauyoyi da jiga-jigan jam’iyyar APC, tun da farko alƙalin ya yi fatali da zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan jihar Umar Tafida, bayan da ya miƙa takardar shaidar makarantar da ya halarta a matsayin shaida.
A game da kura-kuran zaɓe, kotun ta ce kimanin shaidu 17 daga hukumar zaɓe ta INEC sun tabbatar da cewa zaɓen ba shi da kura-kurai kamar yadda jam’iyyar adawa ta PDP ta yi ikirari.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan yanke hukuncin, Lauyan jam’iyyar APC mai mulki, Usman Sulaiman (SAN), ya bayyana cewa, shaidun da ’yan adawar suka kawo manyan maganganu ne na ji don haka ba za a amince da su a kotun ba, don haka ne suka samu nasara, ya kara da cewa, shaidun INEC kimanin 17 daga cikinsu kuma sun shaida cewa zaɓen ba shi da kura-kurai.
Ya kuma buƙaci bangarorin biyu da su haɗa kai domin ci gaban jihar Kebbi, ya kuma bayyana hukuncin a matsayin nasara ga ɓangaren shari’a da kuma al’ummar jihar Kebbi masu son zaman lafiya.
