Kotu ta tasa ƙeyar mutane biyu zuwa gidan yari kan satar kaji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne wata Kotun Shari’a dake Jihar Ogun ta yanke wa wani mai suna Shibu Abdullahi ɗan shakara 21 da Yakubu Usman mai shekaru 25 hukuncin zama a kurkuku na wata guda bisa sace kaji biyu da adadin kuɗinsu ya kai Naira 70,000.

Alƙali O.O. Fadairo ya yanke wa kowane ɗayan su zaman watan ne ba tare da zaɓin tara ba, bayan amsa laifukan da ake tuhumar su a kai.

Lamarin ya auku ne a ranar 30 ga watan Maris, inda matasan tare da wasu suka aikata satar da misalin ƙarfe 2 na dare a No 2 layin Ibukun Oluwa dake yankin Ota a jihar, kamar yadda wani Sufeton ƴan sanda, E.O. Adaraloye ya bayyana .

Ya ce, ɓarayin da ƴan rakiyarsu sun sace kaji biyu na kuɗi N70,000 mallakar wani mai suna Bello Kolawole, wanda hakan ya saɓa wa dokar sata ta jihar ta kundin 2006.

By Babaji