Kotu ta umarci NNPC ya biya Naira miliyan 629 ga ma’aikacin da ya kora

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun ƙoli ta masana’antu ta ƙasa ta bayar da umarnin biyan wani ma’aikacin kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) naira miliyan 629 bisa rashin adalci da kamfanin ya yi masa a shekarar 2018.

Alƙalin Alƙalan Sashen Shari’a na Fatakwal, Mai Shari’a Faustina Kola-Olalere, ta ce korar da aka yi wa mai shigar da ƙara, Dakta Williams daga kamfanin NNPC ya yi daidai da rashin bin dokokin aiki.

An bayyana hakan ne a shafin intanet na kotun masana’antu ta kasa a ranar Litinin.

Williams ya tabbatar da cewa ya yi aiki a matsayin mataimakin mai kula da harkokin gudanarwa na NNPC har zuwa lokacin da aka kori shi ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bukaci kotu da ta umarci a biya shi da diyyar N25,000,000,000.00 saboda karya ƙa’idar kwangila da kuma korar sa ba bisa ƙa’ida ba.

Lauyan mai da’awar, F.K. Amachree Esƙ., ya bayar da hujjar cewa, bayan gano wanda ya aikata zamba a cikin kamfanin, NNPC “ta ɗauki ƙarin matakai a kan Dokta Williams, wanda ya yi aiki sama da shekaru 30 ba tare da wata tambaya ko gargaɗi ba, kuma bai taba saba ƙa’idojin Kamfanoni da ƙa’idoji ba, yin watsi da shawarar kwamitin haɗin gwiwa da kuma korarsa ba zato ba tsammani.”

Lauyan ya ƙara da cewa, bisa ga dokar aiki, kamfanin NNPC ya gaza yin kasala ko kuma gano duk wata hanyar sauraren shari’a ta gaskiya kamar yadda aka tsara a cikin tsarin manufofin kamfanoni da tsarin aiki kafin ya sallami wanda yake karewa.

A ɓangaren ‘yan adawa, ƙungiyar lauyoyin NNPC ta yi zargin cewa korar Williams ta gaskiya ne saboda sakaci da yi wa aiki riƙon sukainar kashi da ya yi, wanda ya janyo hasara mai yawa ga kamfanin.

Lauyan na NNPC ya ƙara da cewa korar Williams ta yi daidai da hukumar NNPC Corporate Policy and Procedure Guide (CPPG), wacce ta bai wa NNPC ikon korar ko soke nazin nasa saboda sakaci, kamar yadda wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Fabrairu, 2018 ta nuna.

Mai shari’a Kola-Olalere ya bayyana cewa kamfanin na NNPC ya gaza tabbatar da laifinsa na aikata laifi ko kuma rashin sakaci a kan tsohon ma’aikacin ba tare da wata shakka ba.

By ukarofi