Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani gogaggen ɗan jarida kuma tsohon babban mai bai wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin yaza labarai, Dr Reuben Abati, a ranar Litinin ɗin da ta gabata ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai je ƙauyensa Daura a jihar Katsina yana raha kan halin da ƙasar nan ke ciki.
Abati ya ce babban abin kunya ne ta fuskar tafiyar da tattalin arziki ga mutanen yankin Kudu maso Yamma da a cewarsa, suka yi ikirarin kwarewa wajen tafiyar da tattalin arzikin ƙasar.
Abati, wanda shi ne jigo a cikin shahararren shirin nan na Arise Tɓ, shirin safe, ya bayyana hakan a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa makomar ’yan Nijeriya a halin yanzu yana tangal-tangal ne, yana mai jaddada cewa raɗaɗin ya yi tsakani fiye da yunwa.
Abati ya ce, “Yanzu an jefa ‘yan Nijeriya cikin matsanancin talauci. Yanzu mun tsinci kanmu cikin rashin tausayi a wani yanayi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yanzu a ƙauyensa Daura da ke Katsina, zai riƙa raha.
“Zai ce, ‘tun da Yarbawa sun ce su suka san tattalin arziki. To, yanzu tattalin arzikin yana hannunsu. Suna tafiyar da shi yadda suka ga dama’.
“Don haka abin da muke fuskanta ke nan. Babban abin kunya ne ta fuskar tafiyar da tattalin arziki ga mutanen da suka fito daga Kudu maso Yamma, suna cewa, ya kamata a sani mutanen Kudu maso Yamma sun fi sanin makamar tafiyar da tattalin arzikin ƙasa’. Mu dai ba mu shaida ba.
“Makarantu sun ƙara kuɗin makaranta. Kun san cewa yanzu tsinken tsire ya koma Naira 1850? Tsinken tsire ma na neman ya fi ƙarfin mu. Duk cikin sarari na mako ɗaya ko biyu. ‘Yan Nijeriya na ƙara gajiya. Dubi Legas da ya kamata a ce cibiyar kasuwancin Nijeriya ce, ta zama kufai.
“Motoci nawa ku ke gani a hanya yanzu? Dole mutane sun canja salon rayuwarsu. Rayuwa ta yi tsada, iyalai da dama na kwana da yunwa.
“Kun san da cewa yanzu mazaje sun fara zuwa kasuwa don tabbatar da cewa matansu ba su ƙara kuɗin cefane a kan abin da aka ba su ba.
“Litar man fetur na zuwa kusan N1200 zuwa N1250 a wasu wurare. Suna neman mu yi sadaukarwa kuma su ba sa sadaukarwa.
“A ƙasar da ake fama da rashin tsaro. Kuma sama da haka, matatar Dangote da NNPCL na jayayya a kan farashin man fetur.
“A sanadiyyar duk waɗannan ruɗani. Makomar mu na tangal-tangal. Kuma raɗaɗin ya wuce yunwa.
“Rayuwa yi matuƙar wahala. Kuma waɗanda ke ikirari, waɗanda suka yi alƙawarin gyara, su suka ɓata.
“Wasu mutane sun ba da sanarwar cewa za su tafi yajin aikin. Za su fita kan titi ranar 1 ga Oktoba saboda zafin yunwa. Ana iya yin rigakafin matsalar.”
