Daga MAHDI M. MUHAMMAD
‘Yan kasuwar man fetur da dama sun damu da jinkirin da aka samu wajen bayyana farashin man fetur, wanda matatar man Dangote ke tacewa, saboda sun lura cewa farashin man da ake shigowa da shi yanzu ya kai kusan Naira 1,120 kan kowace lita.
Dillalan sun bayyana cewa tsadar mai daga matatar Dangote zai sa ’yan kasuwa su shigo da shi daga waje gwamnati ta buɗe kasuwar domin yin gasa.
A watan Yulin wannan shekara ne ƙungiyar masu sayar da man fetud ta Nijeriya ta bayyana cewa kuɗin shigo da mai ya kai Naira 1,117 kan kowace lita.
Yayin da farashin man fetur ya tashi tsakanin N600 zuwa N700 kam kowace lita a watan Yuli, an kuma ƙara kuɗin a makon jiya zuwa tsakanin N855 zuwa N897 lam kowace lita na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, yayin da wasu dillalai masu zaman kansu suka ƙara farashinsu zuwa sama da N1,000.
An kuma tattaro a ranar Litinin ɗin da ta gabata cewa, jinkirin sakin farashin man Dangote ya sa ‘yan kasuwar man suka aara tattaunawa da abokan hulɗar su na aasashen waje a yunƙurin fara shigo da mai daga ƙasashen waje.
