Gwamnati ta dakatar da kuɗaɗen tallafin da ake bai wa jami’o’in Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ba da umarnin cire kuɗazen tallafi na jami’o’in tarayya da cibiyoyin ilimi daga asusun baitul mali.

A wata wasiƙa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa ta aike wa shugabannin jami’o’in, mai ɗauke da kwanan watan 6 ga watan Satumba, 2024, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya miƙa umarnin shugaban ƙasar zuwa ga Ministan Kuzi da Tattalin Arziki na Aasa, Wale Edun, inda ya ba da umarnin a dakatar da ba da tallafin.

Umurnin ya kuma bai wa jami’o’i da cibiyoyin ilimi ’yancin cin gashin kansu don gudanar da asusun asusun tallafin su a bankunan kasuwanci.

Ana sa ran wannan matakin zai inganta cin gashin kan harkokin kuɗi na jami’o’i da cibiyoyin ilimi, da inganta bincike da ƙirƙire-ƙirƙire a ƙasar.

Wasiƙar daga NUC mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin sakataren zartarwa, Chris Maiyaki, ta ce: “Hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa ta samu wannan umarni ne daga mai girma ministan ilimi Ref. DE/HE/37/ɓII/324 kuma mai kwanan wata 4 ga Satumba 2024, yana aika da wasiƙu daga Babban Sakatare zuwa Shugaban ƙasa, Gidan Jiha, da kuma PRES/87/MF/71/198/MBEP/15 da kwanan wata 23 ga Yuli 2024 a kan batun da ke sama.

“Wasiƙar ta isar da umarnin shugaban ƙasa ga Mai girma Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki na cire kuɗaɗen tallafi na jami’o’in tarayya da cibiyoyin ilimi daga asusun baitul mali (Treasury Single Account) (da kuma bai wa jami’o’i da cibiyoyin ilimi ‘yancin cin gashin kansu wajen gudanar da ayyukansu).

By ukarofi