Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Babban Lauyan Nijeriya (SAN) kuma Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Sakandaren Gwamnati na ƙasa, GSS, da ke Maraba, Ilorin, Barista Seni Ibiwoye, ya gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan ka da ya zama silar juyin-juya hali a Nijeriya saboda taɓarɓarewar tattalin arziki.
Ibiwoye ya yi gargaɗin cewa ci gaba da sakaci na iya haifar da juyin-juya hali a faɗin ƙasar tare da sakamakon mara kyau.
Ibiwoye ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a wajen bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar GSS Maraba, a Ilorin, inda kimanin tsofaffin dalibai 80 suka shiga makarantar shekaru 50 da suka gabata. Sanye da kayan makaranta, sama da tsofaffin ɗalibai 50 masu shekaru 60 zuwa 70 ne suka halarci bikin, duk da cewa mambobi 27 na ƙungiyar sun rasu.
A nasa jawabin Ibiwoye ya nuna damuwarsa kan halin da al’ummar ƙasar ke ciki, inda ya ce ’yan Nijeriya na cikin mawuyacin hali.
Ya nanata cewa ra’ayin jama’a game da gwamnati ya kasance marar kyau, ba tare da wani yabo ba.
“Ta hanyar horarwa da hangen falsafa na, koyaushe ina da burin samun fata mai kyau. Kamar yadda suke cewa, ‘In dai akwai rai, akwai fata.’ Abin da nake so in yi bayyana kenan a cikin waɗannan lokutan wahala,” inji Ibiwoye.
“Amma kuma dole ne in amince da tsananin rashin jituwa da ɓacin rai a tsakanin ’yan Nijeriya. Na shaida ɓacin ran mutane a wajen zanga-zanga, kuma na tabbatar da cewa mutane ba su jin daɗin yadda ake mulkar su. Halin da ake ciki yanzu abin takaici ne, amma dole ne mu ci gaba da fatan alheri.”
Ibiwoye ya yi gargaɗin cewa lamarin na iya zamewa cikin halin kaka-nika-yi idan ba a magance matsalar ba.
Ya yi gargaɗi, “Dole ne mu yi taka tsantsan. Zanga-zangar talakawa na iya rikiɗewa zuwa abin da ake kira juyin juya hali, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba. Wannan ya wuce zanga-zangar da NLC ko NAN ta shirya; zai iya haɗawa da kowa, kuma babu wanda zai iya hasashen yadda za a kawo ƙarshensa.”
