
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗɗa na daga cikin dubban mutanen da suka halarci bikin sallar gani a garin Daura da ke jihar.
Sallar Gani tana ɗaya daga cikin bukukuwan da ake yi a kowacce shekara a ƙasar Daura na zagayowar wannan wata mai tsaki da aka haifi fiyayyayen halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Cikin bukukuwan da ake yi akwai hawan Dawaki da Sarkin Daura ya kan jagoranta tare da hakimansa da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya a kowacce shekara.
A jawabinsa, mai martaba sarkin Daura Faruk Umar Faruk ya gode wa gwamna Raɗɗa kan ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na kawo cigaba a masarautar Daura.
Sarkin ya kuma yaba wa gwamnan wajen biyan kuɗin giratuti na waɗanda suka ajiye aiki da biyan ma’aikata haƙƙinsu akan lokaci.
Haka nan, ya taɓo aikace-aikace da dama da gwamnan ya aiwatar cikin ƙanƙanin lokaci, ya na mai jaddada goyon bayan masarautar Katsina da Daura ga gwamnatin Dikko Raɗɗa a ƙoƙarin da ta ke yi wajen haɓaƙa harkokin noma da ilmi da kuma harkar kiwon lafiya.
Ya ce, a fannin tsaro, gwamnan ya ciri tuta, domin a halin yanzu an fara samun zaman lafiya a jihar
A nasa jawabin gwamna Dikko Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta masarautun jihar domin maido da martabar da aka sansu da ita.
Ya kuma yi godiya ga sarakunan Katsina da Daura akan cikkaken haɗin-kai da goyon baya da suke bai wa gwamnatin nasa.
Daga cikin waɗanda suka take wa gwamnan baya akwai shugaban ma’aikatan Fadar gwamnatin jihar, Alhaji Jabiru Tsauri da kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar.
