
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A daidai lokacin da Musulmi ke cigaba da gudunar da murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), shugaban kwamitin majalisar tarayya mai kula da harkokin cikin gida, Hon. Abdullahi Aliyu na taya al’ummar musulmi murna.
Hon. Abdullahi Aliyu (Dujuman Katsina) ya ce, ya na kira ga al’ummar musulmi su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya ga ƙasa baƙi ɗaya.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa ɗan majalisar kan harkar labarai, Frances Sardauna ya fitar inda Dujuman Katsinar ya yi kira ga Al’ummar Musulmi su yi koyi da zaman lafiya da ƙaunar juna da gaskiya da amana da kyautatawa da kuma sadaukarwa irin ta Manzon Allah Muhammad (SAW) a lokacin bikin.
Ya ce, tsananin gaskiyarsa da ƙimar Annabi Muhammad (SAW) ta zama abin koyi ga dukkan musulmi inda ya ce, abu ne da za a yi amfani da su wajen nemawa ƙasa zaman lafiya da tsaro.
Ɗan majalisar, wanda shi ke wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu na iya ƙoƙarinsa, wajen ganin an tsamo Nijeriya daga matsin tattalin arziki
Kazalika, ya yi kira ga ƴan Nijeriya su kasance masu ƙaunar ƙasa da yin addu’o’in samun nasara ga shugabanni.
.
