
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Legas, ta bayyana cewa Rundunar ‘Yan sanda ta aiki bisa saɓa wa doka a lokacin da ta ayyana ɗan gwagwarmaya kuma mawallafin jaridar ShaharaReporters, Omoyele Sowore wanda ake nema ruwa-a-jallo a 2025.
Da yake gabatar da hukunci a ranar Juma’a, Mai Shari’a Musa Kakaaki ya ce matakin rundunar ya saɓa wa hukuncin dokar ƙasa, wanda ya kum faɗaɗa zuwa wulaƙanta ik9n mulki.
Don haka ne kotun ta umarci rundunar, Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun da Kwamishinan ‘yan sanda a Legas, Moshood Jimoh da su biya tarar Naira miliyan 30 na dameji akan ɗan gwagwarmayar.
A cewar alƙalin, babu wani ɗan Nijeriya da za a ayyana a matsayin babban mai laifi saboda aiki da ‘yan bayyana ra’ayi, yin zanga-zangar lumana ko kira ga tabbatar da gaskiya da adalci akan hukumomin gwamnati.
Mai Shari’ar ya kuma soki abin da ya kira da “rashin bin doka” daga ɓangaren kwamishinan ‘yan sandan Legas, inda ya ce wajibi ne Sufeto Janar na ‘yan sanda ya hukunta shi akan haka.
Alƙalin ya ƙara da cewa, ayyana mutum a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo a Nijeriya yanzu yana da buƙatar bin matakan doka masu tsauri.
Ya bayyana cewa, za a yi haka ne idan aka sami izini daga kotu, sanarwa ta hanyoyin da doka ta amince da su da ƙwaƙƙwaran hujjar da ke nuna wanda ake son ayyanawa na ƙoƙarin take doka da gangan.
A ranar 3 wata Nuwamban 2025 Kwamishinan ‘yan sandan Legas ya ayyana Sowore wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sa da yunƙurin shirya zanga-zanga a yankin Third Mainland Bridge bisa ruguza wasu gine-gine a Oworonshoki.
