Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kusanto ta a lokacin ne ‘yan kasuwa musamman masu sayar da kayan masarufi da na marmari ke ƙara farashin kayan su.
Duk da kiraye kiraye da malamai, sarakuna da sauran manyan gari ke yi ga ‘yan kasuwan da su dubi darajar wannan wata su guji ƙara farashin kayan abinci “amma a maimakon su bar farashin yadda yake a lokacin wata mafi daraja suka ƙara farashin,”inji wani malami.
Kan haka ne Gidauniyar Gwagware Musa Adamu tayi tir da Allah wadai tare da kiran gwamnati ta kafa ƙwaƙƙwarar kwamiti da zai zauna da ‘yan kasuwan domin kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi’a na ‘yan kasuwan a jihar.
Shugaban gidauniyar kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira inda ya nuna takaici ganin waɗannan ‘yan kasuwa da al’ummar jihar duk musulmi ne “amma ba sa tashin zaluntar mutane sai lokacin wannan wata mai alfarma”inji Suleiman Funtua.
Ya ce gidauniyar ta yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa kan yadda ya tallafawa mata da masu buƙata na musamman da sauran al’ummar jihar marasa ƙarfi da kayan abinci , sana’o’i, kuɗi a gabannin watan da muke ciki na watan Ramadan.
Haka kuma kwamred Suleiman ya yabawa ‘yan majalisar ƙasa da na jiha da manyan jami’an gwamnati da kuma manya ‘yan kasuwa kan yadda suke taimakawa al’ummar musulmi da tallafi na kuɗi da kayan abinci musamman a yankin Funtua.
Ya bayyana cewa Gidauniyar Gwagware Musa Adamu Funtua ita ma tun kafin a fara azumin watan Ramadan ta rarraba irin wannan tallafi dai dai ƙarfin ta.
Kwamred Suleiman ya ce babu shakka wannan tallafi ya taimaka wa marasa ƙarfi wajan tafiyar da azumi ba tare da shiga cikin damuwa ba
