Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar halascin EFCC da wasu hukumomi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da wasu jihohi 16 suka shigar kan Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) wadda ke ƙalubalantar halascin hukumar EFCC da wasu hukumomi biyu.

Sauran biyun sune hukumar hana rashwa da laifuka masu kama da ita (ICPC) da cibiyar leƙen asiri ɓangaren kuɗi ta ƙasa (NFIU).

Tarin alkalai bakwai ne suka gudanar da hukuncin kan ƙarar wadda suka ce ba ta da nagarta.

Cikin hukuncin da Alƙali Uwani Abba-Aji ta jagoranta, ta warware batutuwa shida da aka zayyano acikin takardar ƙarar inda ta ce dokokin hukumomin hana yin rashawa sun samo asali ne daga Majalisar Ƙasa waɗanda bisa ƙwarewarsu ne suka tabbatar da su.

Ɓangaren shigar da ƙarar ya koka kan cewa dokar EFCC an samo ta ne daga zaman Majalisar Ɗinkin Duniya kan Rashawa wadda mafi yawancin majalisun dokokin jihohin Nijeriya ba su tantance ba kuma ba ta cikin kundin dokar ƙasa ta 1999.

Saidai a yayin hukuncinta, Alƙali Abba-Aji ta ce samar da EFCC ba ta buƙatar tantancewa ko tabbatarwar majalisun dokoki.

Daga nan ne alƙalin ta yi watsi da ƙarar bayan tabbatar da zaman Majalisar Ɗinkin Duniya kan Rashawa a matsayin hujja da ƙasashe da dama suka amince da hukuncinsa.

By Babaji