
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙaramin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle ya maka wasu manyan ƴan jaridun yankin Arewa, Shua’ibu Mungadi da Tijjani Ramalan a kotu bisa zargin ɓata masa suna.
An shirya takardar ƙarar ne wadda aka miƙa gaban Alƙali Musa Ahmad na Babbar Kotun Tarayya dake Kano inda aka zayyano ƴan jarida biyu da kamfanin jarida na Vision da Vision FM da gidan telebijin na Farin Wata da kuma Liberty rediyo da talabijin a matsayin waɗanda aka shigar da su ƙara.
Matawalle ya buƙaci a biya shi Naira biliyan 10 daga kowane ɗaya daga cikin ɓangarori shida da ake tuhuma a matsayin kuɗin damejin da aka yi masa.
Ministan, kamar yadda ya buƙaci kotun a cikin ƙarar, ya nemi a dakatar da baki ɗaya ɓangarorin daga wallafawa, ko ruwaito wani abu da ya shafe shi ko ofishinsa daga yanzu har zuwa lokacin da za a yi hukunci game da ƙarar.
Haka nan cikin wata takarda da ke goyon bayan ƙarar, wadda mai taimaka wa ministan na musamman, Alhaji Masudu Abdulƙadir ya fitar, ya ce a matsayin Matawalle na gwamnan Zamfara tsawon shekaru huɗu, ya yi ta ƙoƙarin magance ta’addanci da ya addabi jihar. Ya na mai cewa daga na uku zuwa na shida cikin waɗanda ake zargin, sun bai wa na ɗaya da na biyu damar yaɗa shirye-shirye tun daga watan Janairun 2024, da suka ƙunshi ƙarairayi, cin fuska, ɓata suna da zargin Matawalle da ɗaukar nauyin ƴan bindiga da ayyukansu a Arewa-maso-Yamma ciki har da Zamfara.
Bugu da ƙari, takardar ƙarar ta kuma buƙaci a dakatar da duka ɓangarorin sake yin wata magana da ta shafi ministan da ke ɗauke da cin mutunci ko ɓata masa suna.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2024.
A kwanakin baya ne mambobin ƙungiyar masu kishin jami’yyar APC suka gudanar da zanga-zanga a Hedikwatar hukumar SSS kan cewa a binciki Bello Matawalle bisa zargin alaƙa da ƴan bindiga.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Musa Mahmud ya yi kira ga SSS da ta yi binciken don kare martabar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hukumomin tsaro daga zargi.
Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya yi irin kiran, tare da neman Matawalle da ya yi murabus daga muƙaminsa inda ya zargi tsohon gwamnan da bai wa ƴan ta’adda mafaka a gidan gwamnati da kuma biyan su kuɗin fansa ta asusun Gwamnatin jihar.
Har’ilayau, Gwamna Dauda ya ce ya kai ƙarar Matawalle ga Mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu da kuma gabatar masu da wasu hujjoji.
