
Daga BELLO A. BABAJI
Aƙalla daraktoci 19 cikin 38 ne da suka rubuta jarrabawar cantatar zama babban sakatare da Ma’aikatar ma’aikata ta shirya suka yi rashin nasara.
Cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Dakta Emmanuel Meribol a madadin kwamitin jarrabawar kuma daga ofishin Shugaban Ma’aikatar ma’aikata (OHCSF), an rubuta jarrabawar ne a ranar Litinin da ta gabata.
19 daga ciki sun yi nasarar cin jarrabawar wanda hakan ya ba su damar hayewa zuwa zagaye na gaba.
An kuma gudanar da mataki na gaba a ranar Laraba wanda a ɓangaren amfani da kwamfuta aka yi shi.
Daga nan ne sai mataki na ƙarshe inda ake sa ran waɗanda suka yi nasara, su ne za a bai wa muƙaman inda za su wakilci wasu ɓangarorin ƙasa akan wasu muhimman abubuwa.
