Jami’ar Kogi ta sallami wasu lakcarori huɗu bisa laifin cin zarafi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’ar Tarayya dake Lokoja a Jihar Kogi ta tabbatar da korar wasu malamai huɗu bisa laifukan saɓa ƙa’idojin jarrabawa da ayyukan lalata.

News Point ta ruwaito cewa, tawagar shugabanci ta Jami’ar ne ta yi hukuncin hakan a zamanta na ranar Alhamis.

Hakan na zuwa ne bayan bincike da aka yi game da matsalolin satar jarrabawa da cin zarafi da aka tuhumci lakcarorin da aikatawa a shekarar da ta gabata.

Tawagar shugabancin wadda Sanata Victor Ndoma-Egba ke shugabanta, ta yaba wa hukumar gudanarwar jami’ar bisa bin ƙa’idodin da suka dace wajen gudanar da binciken.

Ya kuma ce ba za su amince da wani rashin biyayya ga dokar Jami’ar ba. Yana mai kira ga jami’ar da ta gaggauta fitar da sakamakon sauran binciken da aka gabatar mata akan ire-iren ayyukan.

By Babaji