Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kotun Ɗaukaka ƙara a Abuja, ta jingine hukuncin wata Babbar Kotun Tarayya dake Kano tare da ayyana shi a matsayin wanda aka soke shi baki ɗaya.

A wani hukunci kashi uku da tawagar alƙalai uku suka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Biobele Georgewill, sun ce babbar kotun ba ta da ikon karɓa ko sauraron kesa-kesan da suke da alaƙa da hukumomin zaɓe na jihohi da cancantar mambobinsu.

Kotun Ɗaukaka ƙarar ta karɓi ƙarar da Antoni Janar na jihar da majalisar dokoki ta jihar da hukumar zaɓe (KANSIEC) suka shigar a gabanta na neman sake yin hukunci kan zaɓen ƙananan hukumomin jihar, wanda hakan ya yi sanadin soke waɗanda aka shigar wa Babbar Kotun Tarayyar na neman iko, tana mai cewa wadda ke da alhaki da ikon karɓar ƙarar ita ce Babbar Kotun jihar.

Haka kuma, Kotun Ɗaukaka ƙarar ta janye hukuncin Babbar Kotun Tarayyar ta Kano na ƙin karɓar jaddawalin ƴan takara daga Jam’iyyar NNPP na tafiyar Kwankwasiyya game da zaɓukan ƙananan hukumomin jihar da suka gabata.

A yayin jagorantar tawagar shari’a na NNPP, Dakta Rilwanu Umar SAN ya nuna jajircewa da ƙwarewa wajen tunkarar shari’ar.

Dakta Rilwanu, wanda tsohon masanin harkar shari’a ne, ya tsayu wajen tabbatar da gaskiya da adalci a yayin shiryawa da gabatar da ƙarar.

Ya bayyana hukuncin a matsayin abinda suka gamsu da shi kuma abinda al’umma suke buƙata, yana mai cewa yanzu Kano tana cikin aminci da kwanciyar hankali bisa gagarumar nasarar.

By Babaji