Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya sake caccakar ‘yan majalisun dokokin ƙasar wanɗanda ya bayyana su a matsayin mafi munin da aka taba gani, bayan Jamhuriyar ta ɗaya da biyu da kuma ta uku.
Obasanjo ya bayyana kuɗaɗen da ‘yan majalisun na jihohi da na tarayya ke karɓa da sunan ayyukan mazaɓu a matsayin fashi da kuma yunƙurin su na tattara kuɗaɗen da ba na halal ba.
Blueprint Manhaja ta ruwaito Obasanjon a littafin da ya wallafa yana cewar, sau biyu ya na karo gaba da gaba da ‘yan majalisun a matakin ƙasa, kuma ya fahimci cewar ba mutane ne waɗanda za su sauya ba, domin gina Najeriyar da ake buƙata.
Tsohon shugaban ya bayyana yadda ‘yan majalisun suka yi ruwa da tsaki wajen hana kafa Hukumar EFCC a lokacin sa, abinda ya kai ga sama da shekara guda suna zaune a kan dokar da ya gabatar musu, kafin su rage mata karfi a kan yadda aka gwamnatin sa ta tsara ta.
Obasanjo ya ce wasu daga cikin su, sun ce muddin suka amince da ƙudirin dokar yadda ya kai ta Majalisar, to za ta buɗe kofar jefa su a gidan yari da zaran sun kammala wa’adin su na majalisa.
Tsohon shugaban ya ce dole ya rattaba hannu a kan abinda ya iya samu daga wurin su na dokar, domin mayar da ita majalisar na iya kashe ta baki ɗaya.
Obasanjo ya ce bayan dokar EFCCn, akwai wasu dokoki da dama da ‘yan majalisun suka yi abinda suke so, wajen sanya muradun su, ba tare da la’akari da ƙasa baki ɗaya ba, ciki harda dokar da ta kafa Hukumar NDDC dake kula da yankin dake da arzikin man fetur.
Tsohon shugaban ya ce dokar ƙasa ta bai wa hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta RMAFC sanya albashin ma’aikata, amma ‘yan majalisun Najeriya sun sanya ƙafa sun shure dokar, wajen rubutawa kan su albashin da suke so, abinda ya sa suka zama na farko ko kuma waɗanɗa suka fi karbar albashi mai toska a ƙasashe maso tasowa na duniya da ma wasu ƙasashen da suka ci gaba.
‘’Lokacin da na ke shugaban ƙasa na ki sake kasafin kuɗin da ban gamsu da shi ba, abinda ya kai ga barazanar tsige ni daga kujera ta, amma hakan bai sa na fasa aniyata ba. Idan suna da ƙarfin karya doka, ni ma ina da ƙarfin rufe asusun kuɗin jama’a domin hana sace su daga ‘area boys’.’’
A kwanakin baya Obasanjo ya ce fatarsa kafin ya mutu, ita ce ganin Najeriya ta samu ci gaban da take bukata, amma kuma ga alama har yanzu da sauran rina a kaba.
