Kuɗin makamai: Rashin takardun sahalewa ya kare Jonathan daga kamun EFCC – Magu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Malam Ibrahim Magu, ya bayyana dalilan da suka sa ba a taba gayyatar tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan domin yi masa tambayoyi kan shahararriyar badaƙalar kuɗin makamai ta dala biliyan 2.1 ba, wadda ta tayar da ƙura a Nijeriya bayan zaɓen 2015.

Magu ya ce, binciken EFCC ya nuna cewa takardun da aka tattara tare da bayanan cikin gida sun tabbatar da cewa kuɗaɗen ba su samu sahalewar hukuma ba domin amfani da su wajen kamfen, lamarin da ya sa ya zama abu mai wuya a ɗora wa Jonathan alhakin kai tsaye.

A cewarsa, rashin sahalewar rubutacciyar umarni ya kawo cikas wajen haɗa hujjar da za ta kai ga gayyatarsa.

Wannan bayani ya fito ne a cikin sabon littafi mai suna “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dokta Charles Omole ya rubuta. An ƙaddamar da littafin ne a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya yi tsokaci kan rayuwa, aikin soja da kuma tafiyar siyasar marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Marubucin ya bayyana cewa yadda aka tafiyar da kuɗaɗen makaman ya janyo tashin hankali mai tsanani a cikin jam’iyyar PDP da kuma gwamnatin Jonathan, musamman tsakanin tsohon Mashawarcin Tsaro na ƙasa, Sambo Dasuki, da wasu manyan jami’an gwamnati.

A cewarsa, taruwar ikon sayen makamai da wasu muhimman ayyukan tsaro a ofishin NSA ya sa wasu ‘yan siyasa ke kallon Dasuki a matsayin “shugaban ƙasa na biyu” tare da Jonathan.

Omole ya ƙara da cewa, fara binciken EFCC ya girgiza jam’iyyar PDP, inda aka riƙa gayyatar manyan shugabannin jam’iyyar domin amsa tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗaɗen makamai zuwa ayyukan siyasa.

Zuwa farkon shekarar 2016, tsohon shugaban PDP na ƙasa, Adamu Mu’azu, ya shiga buya bayan jami’an bincike sun fara nemansa. Haka kuma, tsohon kakakin jam’iyyar, Olisa Metuh, ya shiga hannun hukuma bayan zargin karɓar naira miliyan 400 daga cikin kuɗaɗen, inda kalamansa na cewa ya fi so ya yi yunwa da ya maido da kuɗin suka zama abin tunawa a wancan lokaci.

Rahoton ya kuma ambaci kama tsohon Darakta Janar na NIMASA, Patrick Akpobolokemi, wanda daga baya ya tsere da belin da aka ba shi kafin a sake cafke shi. Lauyan da ya tsaya masa ya shiga tsare, yayin da shugabannin yankuna shida na PDP suka ce ba su san asalin kuɗaɗen da jam’iyyar ta yi amfani da su ba.

A lokacin da aka tambayi Magu kan yiyuwar gayyatar Jonathan, tsohon shugaban EFCC ya jaddada cewa hujjojin takardu sun nuna cewa kuɗaɗen ba su da sahalewar amfani da su a kamfen, don haka ba a samu ginshiƙin doka na kiran tsohon shugaban ƙasa ba. Magu ya kuma yi ƙorafi kan yadda manyan ‘yan siyasa ke amfani da manyan lauyoyi da kuɗaɗen shari’a domin daƙile gurfanar da su gaban kotu.

Bugu da ƙari, littafin ya bayyana cewa bisa shawarwarin Kwamitin Binciken Sayen Makaman Soja, Shugaba Buhari ya umurci EFCC da ta binciki manyan jami’an soja 17, ciki har da tsofaffi da masu aiki, musamman daga Sojojin Sama. Daga bisani, marigayi Air Chief Marshal Aleɗ Badeh ya fuskanci tuhume-tuhume na safarar kuɗi, cin amana da rashawa, ciki har da zargin karkatar da naira biliyan 1.4 domin sayen katafaren gida a Abuja.

A ƙarshe, littafin ya buɗe sabon shafi kan ɗaya daga cikin manyan badaƙalar cin hanci a tarihin Nijeriya, yana bayyana rikice-rikicen cikin gida, matsalolin shari’a da kuma sarƙaƙiyar siyasa da suka yi tasiri ga yadda EFCC ta tafiyar da binciken badaƙalar makaman.

By ukarofi