Tinubu na gamsuwa da jagorancinka a Ribas – Ribadu ga Fubara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai Bai Wa Shugabab ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro na ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na nuna cikakken gamsuwa da salon jagorancin Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, yana mai jaddada cewa irin yadda yake tafiyar da al’amuran tsaro da siyasa a jihar ya cancanci yabo.

Ribadu ya faɗi hakan ne a ranar Litinin yayin da ya jagoranci wata tawagar fadar shugaban ƙasa zuwa Zauren Gwamnatin Jihar Ribas da ke Fatakwal.

Tawagar ta ƙunshi Ministan Ayyuka, David Umahi, Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, da manyan jami’an Kamfanin Man Fetur na ƙasa, NNPC.

A cewar Ribadu, Jihar Ribas na daga cikin jihohin da ke more zaman lafiya a ƙasar nan, duk da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassa. 

Ya ce, dalilin ziyarar tawagar shi ne ƙara ƙarfin gwiwar ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Ogoni.

Ribadu ya bayyana cewa, “wani sabon babi na farfaɗowa” na buɗewa a Ogoni, yana mai nuna fata cewa Nijeriya za ta fi samun ci gaba idan aka fara sauye-sauye daga wannan yanki.

Ya ce, Shugaba Tinubu ya umurce shi da ya isar da saƙon godiya ga Gwamna Fubara bisa jagoranci da daidaitaccen tsari da yake nunawa, musamman dangane da tattaunawar dawo da ayyukan haƙar mai a Ogoni.

Ya kuma yaba wa al’ummar Ogoni bisa goyon baya, haƙuri da fahimta da suke nunawa a wannan muhimmin lokaci, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen samar da yanayi mai kyau na zaman lafiya da ci gaba.

Ribadu ya ƙara jinjinawa gwamnatin jihar bisa samar da harabar Jami’ar Muhalli da kuma karɓar baƙuncin Ofishin Yankin Kudu maso Kudu na Ofishin Mashawarcin Tsaro na ƙasa.

A kwanakin baya dai Gwamna Fubara ya koma jam’iyyar APC mai mulki, matakin da ya zo ne bayan Shugaban Majalisar Jihar Ribas, Martin Amaewhule, da ‘yan majalisa 16 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar. Gwamnan ya bayyana cewa sauya jam’iyyar da ya yi na da nufin mara wa Shugaba Tinubu baya domin ci gaban ƙasa.

By ukarofi