Ku nemi watan Shawwal ranar Asabra, Sarkin Musulmi ga Musulmin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli na Harkokin Musuluncin Nijeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga Musulmin Nijeriya da su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Asabar, 30 ga Afrilu.

Sarkin Musulmi ya buƙaci a nemi watan ne biyo bayan shawarar da Kwamitin Neman Wata (NMSC) ya bayar, kamar dai yadda darakta a NSCIA, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, ya bayyana.

Basaraken ya ce, duk inda aka samu ganin jinjirin watan Shawwal, a hanzarta a sanar da sarakuna da ‘yan kwamitin duban wata (NMSC) don a sanar da al’umma.

A cewar Usman, “Muddin aka samu labarin ganin wata daga wajen Musulmin kirki, Sarkin Musulmi zai tabbatar da ranar Lahadi, 1 ga Mayun 2022 a matsayin 1 ga Shawwal kuma ranar Sallah Ƙarama (Idul Fitr).
“Idan kuwa ba a ga wata ba a wannan rana, shi kenan sallah ta tabbata ranar Litinin, 2 ga Mayu, 2022.”

Kazalika, Sarkin Musulmi ya ƙarfafa wa Musulmi batun fitar da Zakkar Kono ( Zakatul Fitr) don amfanin marasa galihu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *