Ku nisanci zanga-zanga, inji jagoran CAN ga Kiristoci

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen jihar Nija ta yi kira ga mabiyanta cewa kar su shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da za a yi a watan Agusta.

Shugaban CAN na jihar, ‘Bishop Bulus Yohanna ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ne cewa wasu kan iya amfani da zanga-zangar wajen tada fitina da za ta iya shafar waɗanda basu-ji-ba basu-gani-ba.

Yohanna ya kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da cewa, baya ga rarraba tallafi, akwai buƙatar a yi aiki kan farashin kayayyaki wanda hakan ya haifar da tsadar rayuwa ƙasar da kuma batun da ya shafi rage kuɗin man fetur.

Bugu da ƙari, ya yi kira ga shugabanni coci-coci da wakilan ƙananan hukumomi da iyaye da su jaddada wa mabiyansu kan kauce wa shiga zanga-zangar saboda zaman lafiya.

By Babaji