
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana matsayarsa game da zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe A wata Agusta.
A lokacin da ya ke magana bayan wani zama da gwamnan Jihar Abia, Alex Otti a ranar Lahadi, Obi ya ce masu zanga-zangar sai sun tabbatar da kiyaye doka da oda, ya na mai kira ga hukumomin tsaro cewa su bi umarnin doka, domin duk duniya an halatta yin zanga-zanga.
Wannan shi ne karo na farko da Obi ya magantu kan zanga-zangar.
Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin labaru, Bayo Onanuga ya alaƙanta Obi da zanga-zangar inda ya ce magoya bayan Obi na shirin tada fitina a Nijeriya.
Sai dai, Obi ya musanta hakan inda ya buƙaci Onanuga ya nemi yafiyarsa a cikin kwanaki uku, ya na cewa rashin yin hakan zai sa a ji su a kotu.
Zargin Onanuga kan Obi ya karaɗe kafafen sadarwa inda kawo yanzu bai nemi yafiyar da Obi ya buƙaci ya yi ba.
