(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
A ci gaba da bayyani kan yadda za a iya ba wa jiki kulawa a lokacin sanyi, a yau darasin namu zai taɓo ɓangaren gashi. Sai dai kafin nan zan so mu yi waiwaye don tunatar da mai karatu abinda darasin namu ya ƙunsa a baya.
Mun soma da bayanin yadda fata ke shiga mawuyacin hali a lokutan sanyi, wanda muka ce da taimakon sanin yadda ake iya kula da ita, za a samu sauƙi daga irin lalacewar da ta ke yi a lokacin sanyi. Sannan mun kawo hanyoyin da za a iya kula da fatar daga ababen ci da na amfani, kafin mu dira kan ƙafa wadda ita ma na ɗaya daga cikin wuraren da ke jigata a lokacin sanyi. Wanda a nan ne muka dasa aya a satin da ya gabata.
Gashi: Babu wani lokaci da gashi ya fi buƙatar kulawa kamar lokacin sanyi, domin a lokacin ne ya fi yawan karyewa da kuma saurin bushewa. Duk da cewa ababen da muke ci ne ababe mafi rinjaye da suke tasiri a gyaruwa da kuma lalacewar gashin kanmu, wannan na daga dalilan da ya sa ingantaccen abinci da kayan itace ke layin farko na bayani ga wadda ta ce tana son gashinta ya gyaru. Sai dai yanayi ma na taka tasa rawar a lokuta da dama, don haka yake da matuƙar muhimmanci a yi amfani da waɗannan matakai a lokacin sanyi don ba wa gashi agaji;
Shan ruwa: kaɗan daga cikinmu ne kaɗai suka san yawan shan ruwa a lokacin sanyi na rage yawan karyewar gashi.
Turara gashi: abinda bature ke kira da ‘steaming’, wanda ake amfani da na’uwa mai sakin zafi ana turare gashin, kuma abu ne mai sauƙin kuɗi ko a wurin jingar yin sa a wuraren gyaran kai. Matuƙa yana taimakon gashi a irin wannan lokaci na sanyi.
Yawan shafa mai: Kasancewar lokacin sanyi na saurin busar da jiki, gashi na buƙatar mai mai matsƙi da zai sa ya zama a jiƙe a kodayaushe, don gujewa abinda zai iya sa ya dinga zuba.
Rufe kai: yawan saka ɗankwali ko hula na da matuƙar muhimmanci ga wadda take son ba wa gashinta kariya daga sanyi. Wannan zai taimaka wurin hana shi ƙara bushewa, tare da hana ƙwayoyin cuta da ka iya illa da iskan hunturu zai kwaso ya kai ga gashin.
Yin kitso: ba abu mai kyau ba ne zama da kai babu kitso a lokacin sanyi, domin iska ya fi samun shiga sosai idan kan yana a tsefe. Sannan za a fi yawan taje shi Idan babu kitso, don haka yawan zubar sa zai fi na idan an kitse shi.
