An sako tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin El-Rufa’i bayan kwanaki 50 a tsare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon shugaban mai’aikatan gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, Bashir Sa’idu ya fito daga hannun hukuma, bayan tsare shi da aka yi na tsawon kwanaki 50 kan zargin sa da hannu a almundahana.

El-Rufa’i ya bayyana hakan ta kafar X a ranar Laraba, inda ya bayyana tsare shi a matsayin abinda aka yi ba bisa adalci ba da kuma siyasantar da lamarin.

Ya ce, Bashir Sa’idu abokinsa ne na tsawon sama da shekaru 53, wanda kuma sun yi karatu a Kwalejin Barewa ta Zariya tare kuma tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi da kuɗi.

El-Rufa’i ya bayyana hakan a matsayin dalilin tsare shi, ya na mai cewa za a san waɗanda ke da hannu a cikin haka zuwa nan da zaɓen 2027.

Ana zargin Sa’idu ne da hannu a rashawa bisa karɓar Naira miliyan 155 da hawa kansu daga wani Muktar a shekarar 2022 inda Hukumar Hana Rashawa da Laifuka masu Kama da ita ta ICPC, ta bayyana hakan a matsayin saɓa wa doka da kuma dalilin tsare shi.

By Babaji