
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta maka Kamfanin Binance Holdings Limited a Babbar Kotun Tarayya don neman a biya ta Dala biliyan 79.51 da Naira miliyan 231 bisa zargin kamfanin da haddasa mata asara.
Haka kuma a cikin ƙarar, Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta nemi kotun da ta tilasta kamfanin ya biya Dala biliyan 2.001 na harajin shekarun 2022 da 2023.
Hallau FIRS ta ce, manyan jami’an kamfanin biyu, wato Trigram Gambaryan da Nadeem Anjarwalla sun haddasa wa tattalin arziƙin Nijeriya asara sakamakon rashin yin rajista da hukumar.
An shigar da Binance ƙara ne sakamakon aikata laifukan ƙin biyan haraji da almundahana da karya ƙa’idodin cinikayyar ƙasa-da-ƙasa.
EFCC da FIRS ne suka shigar da Binance ƙara a kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Emeka Nwite sakamakon ƙarya dokokin kamfani da na haraji da sauransu.
