Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Kungiyar Alƙalai ta Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da lambar yabo a matsayin uban ƙungiyar na ƙasa, saboda ƙoƙarinsa na tallafa wa addinin Musulunci da kuma inganta harkokin shari’a a jihar.
Shugaban ƙungiyar, Alƙali Mudassir Hassan, wanda ya jagoranci tawagar zuwa gidan gwamnatin jihar, ya bayyana cewa sun ziyarci gwamnan ne domin jaddada goyon bayansu gare shi, tare da miƙa masa lambar girmamawa bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa shari’a, da kuma inganta walwalar alƙalai.
Ya nuna gamsuwarsa da salon mulkin Gwamna Namadi, yana mai cewa gwamnatin ta bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen horar da alƙalai domin su ƙara kwarewa a aikinsu.
Alƙali Mudassir ya roƙi gwamnatin Jigawa da ta taimaka wa ƙungiyar wajen samar da mota domin gudanar da ayyukan ƙungiyar, tare da gyara sakatariryarsu da ke bukatar sabuntawa domin su ci gaba da gudanar da aikinsu yadda ya dace. Haka kuma ya yi kira ga sauran gwamnonin ƙasar su yi koyi da manufofin Gwamna Namadi wajen kare martabar Addini da shari’a.
Daga cikin manyan jami’ai da suka halarci bikin akwai Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Auwal Sankara, wanda ya bai wa ƙungiyar alƙalai gudunmawar naira miliyan biyu a madadin gwamnatin jihar.
A cikin jawabinsa, Gwamna Umar Namadi ya yi alkawarin gyara ofishin ƙungiyar Alƙalai tare da duba batun samar musu da motar aiki, domin ƙara inganta aikinsu a fadin jihar.
