Tinubu ya rantsar da Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaron Rundunar Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro na ƙasa.

An gudanar da rantsarwar ne a ranar Alhamis a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan Majalisar Dattawa ta amince da naɗinsa a hukumance a ranar Laraba, sakamakon tantancewar da ta ɗauki kusan awanni biyar ana yi masa.

A yayin tantancewar da ‘yan majalisar suka yi masa, Janar Musa ya fuskanci tambayoyi masu tsauri kan taɓarɓarewar tsaro a wasu sassan ƙasar nan, ciki har da janyewar sojoji daga makarantar ‘yan mata ta gwamnati da ke Maga a Jihar Kebbi, jim kaɗan kafin sace ɗaliban makarantar a ranar 17 ga Nuwamba.

Da yake amsa tambayoyin, sabon Ministan Tsaron ya sha alwashin kafa cikakken kwamitin bincike da zarar ya kama aiki domin zaƙulo gaskiyar dalilin janyewar sojojin da kuma gano duk wanda ke da hannu a abin da ya faru.

Ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci sakaci ko gazawa a fannin tsaro ba, musamman idan hakan ya jawo salwantar rayukan ‘yan ƙasa.

Haka nan kuma Janar Musa ya tabbatar da cewa zai gudanar da cikakken bincike kan kisan Kwamandan Bride, Birgediya-Janar Musa Uba, a Jihar Borno, tare da sauran hare-haren da aka kai wa manyan jami’an sojoji a ‘yan kwanakin nan, inda ya ce wajibi ne a tabbatar da gaskiya ta fito fili domin ɗaukar matakin da ya dace.

Nazin Janar Musa ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, wanda aka ce ya yi ne sakamakon dalilan rashin lafiya.

Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa an zaɓi sabon Ministan Tsaron ne bisa kwarewarsa, gogewarsa a aikin soja, da kuma tarihin jajircewa wajen kare ƙasa.

Masu sharhi na tsaro na kallon naɗin Janar Musa a wannan lokaci a matsayin wani mataki na ƙarfafa tsarin tsaron Nijeriya, musamman duba da yadda ƙasar ke fuskantar ƙalubale daga ta’addanci, fashi da makami, da sauran nau’o’in manyan laifuka.

Ana sa ran sabon Ministan Tsaron zai taka rawar gani wajen sake tsari, farfaɗo da kwarin gwiwar sojoji, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro daban-daban domin dawo da cikakken zaman lafiya.

Akan hakan dai, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bayan tabbatar da Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin Ministan Tsaron Nijeriya da Majalisar Dattawa ta yi.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis ta shafinsa na ɗ (wanda aka fi sani da Tiwita), inda ya yaba wa Majalisar Dattawa kan tabbatar da Musa cikin gaggawa.

Ya lura cewa, ‘yan majalisar sun kammala aikin cikin awanni arba’in da takwas bayan miƙa sunansa ga Majalisar Dokoki ta ƙasa don tantancewa da tabbatarwa. A cewar Tinubu, Musa zai zama Ministan Tsaro a wani mawuyacin lokaci a cikin yanayin tsaron Nijeriya.

Ya rubuta, “Kwanaki biyu da suka gabata, na mika sunan Janar Christopher G. Musa, tsohon Babban Hafsan Tsaronmu kuma mutumin kirki, ga Majalisar Dattawan Nijeriya don tabbatarwa a matsayin Ministan Tsaron Tarayya. Ina so in yaba wa Majalisar Dattawan Nijeriya saboda hanzarta tabbatar da Janar Musa jiya. Naɗinsa ya zo ne a wani mawuyacin lokaci a rayuwarmu a matsayinmu na ƙasa. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.”

Naɗin Janar Christopher Musa da kuma tabbatar da shi daga baya sun samu yabo daga ‘yan Nijeriya da dama, ciki har da masu sharhi kan tsaro waɗanda suka ce yana ɗaya daga cikin mafi kyawun naɗe-naɗen da Shugaba Tinubu ya yi tun lokacin da ya hau mulki a 2023.

Sabon Ministan Tsaro, wanda zai cika shekaru 59 a ranar 25 ga Disamba, soja ne mai hazaƙa wanda ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa Oktoba 2025.

A shekara ta 2021, an naɗa Janar Musa Kwamandan, Operation Haɗin Kai. Daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya kafin Shugaba Tinubu ya naɗa shi Babban Hafsan Tsaro a 2023.

By ukarofi