Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mutane a Safana sun yi wa Sanatan Arewa ta Tsakiya ihun ‘ba ma yi’. Wannan lamari ya faru ne a garin Safana a Jihar Katsina, inda Gwamna Dikko Raɗɗa yake kai ziyarar aiki a ƙananan hukumomi da ke jihar.
Yayin da yake jawabi a wajan taron ƙaddamar da wasu kayayyaki ya sanar da kyautar littafin rubutu guda 3,000 da Sanata Abdul’aziz Musa Yar’Adua, wanda yake wakiltar Katsina ta Tsakiya, sai dai nan take mutanen da ke wajen suka kama ihun “ba ma yi! Ba ma yi”.
Wasu daga cikin waɗanda Wakilin Blueprint Manhaja ya tattauna da su sun ce, sun yi haka ne domin su nuna damuwa ga sanatan kan rashin taɓuka musu komai a mazaɓarsa.
“Muna neman tallafin karatu, muna neman aikin yi da tsaro, meye za mu yi da littafin rubutun ’yan firamare,” inji wani ɗan asalin ƙaramar Hukumar Safana.
Wani cewa ya yi “Idan ka ga Sanatan a garin Safana, to ya zo ɗaurin aure ko gaisuwar mutuwa.”
Wasu daga cikin kayayyakin da ƙaramar hukumar ta samar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar sun haɗa da keken ɗinki guda 100 da injin markaɗe guda 100. Sauran sun haɗa da injin taliya guda 100, injin huɗa 100 da injin niƙa guda 100. Akwai kuma baburan hawa 50, motoci 10 da motar bus guda ɗaya da kekunan guragu guda 60. Haka kuma ƙaramar hukumar ta bai wa mata 101 tallafin kuɗi, suna da maza matasa da kuma mabuƙata suma sun amfana da tallafi na kuɗi. Su ma shugabannin ‘ya’yan jam’iyyar APC 297 a ƙaramar hukumar su ma sun amfana da tallafi na kuɗi.
