Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayyana cewa batun cikakken ‘yancin kai ga ƙananan hukumomi ya zama gaskiya a faɗin jihar, yana mai cewa wannan ci gaba ne mai matuƙar muhimmanci ga bunƙasar ci gaban karkara.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin wani shirin tallafa wa al’umma da ƙaramar Hukumar Daura ta shirya, wanda aka gudanar a garin Daura a ranar Laraba.
A cewarsa, wannan mataki wani juyin-juya-hali ne da zai buɗe sabon babi a harkokin mulki da ci gaban al’umma a matakin ƙasa.
Ya ƙara da cewa, tun daga ranar 24 ga watan Nuwamba a ƙaramar Hukumar Faskari, inda aka fara wannan shirin tallafa wa al’umma, dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar ke karɓar kuɗaɗensu na wata-wata ba tare da tsaiko ba.
Radda ya jaddada cewa shugabannin ƙananan hukumomin za su iya ba da shaida cewa a kowane wata gwamnati na sakin kuɗaɗen da suka dace da su ba tare da jinkiri ba.
Gwamnan ya kuma bayyana karɓar rahoton ayyukan da ƙaramar Hukumar Daura ta aiwatar tun bayan fara sakin kuɗaɗe cikin gaggawa, yana mai nuni da cewa hakan ya ƙara hanzarta ayyukan raya ƙananan hukumomi.
A ɓangaren shirin tallafa wa al’umma a Daura, Gwamna Radda ya ce an raba N50,000 ga kusan manyan masu ruwa da tsaki 20, yayin da mutane 616 kuma za su karɓi N20,000 kowannensu.
Hakazalika, za a raba injinan ɗinki 40 ga mata, babura 24, da injinan tura ruwa 40 don bunƙasa sana’o’i da noma.
A fannin kiwon lafiya kuma, gwamnan ya sanar da cewa an miƙa Babban Asibitin Daura ga Gwamnatin Tarayya, inda aka mayar da shi Federal Medical Centre Daura.
Haka nan, gwamnatin jihar ta riga ta bayar da kwangilar gina sabon asibitin janar a Daura, wanda ake sa ran kammalawa a shekarar 2026.
A ziyarar da ya kai wurare daban-daban na ayyuka a Daura, gwamnan ya duba ci gaban gine-ginen hanyoyi da cibiyoyin al’umma, sannan ya ƙaddamar da aikin ring road da kuma babbar hanyar da ke kaiwa Fadar Sarkin Daura.
Rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya nuna cewa shirin tallafa wa al’umma a Daura wani ɓangare ne na gagarumin shirin da aka fara tun ranar 24 ga watan Nuwamba a Faskari, wanda ya shafi dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina.
