Majalisar Tattalin Arziki ta amince da biliyan N100 don gyaran cibiyoyin horar da jami’an tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC), ta amince da ware Naira Biliyan 100, bisa jiran sahalewar Shugaban ƙasa Bola Tinubu, domin gudanar da cikakken aikin gyara da farfaɗo da cibiyoyin horas da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin Nijeriya.

Matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin wucin-gadi da aka kafa domin duba halin da cibiyoyin horas da jami’an tsaro ke ciki a ƙasa. 

Haka kuma, a taron ta na 154 da aka gudanar ta hanyar zamani, wanda Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta, majalisar ta kuma amince da Naira Biliyan 2.6 domin kuɗin ayyukan tuntuɓa (consultancy) da za su goyi bayan shirin.

Tun a taron majalisar na 152 da aka gudanar a watan Oktoba, Shugaban ƙasa Tinubu ya gabatar da buƙatar sake fasalin makarantu da cibiyoyin horas da jami’an tsaro a faɗin ƙasar, domin ƙara inganci da kwarewar rundunonin tsaro.

Shugaban kwamitin wucin-gadin da ya yi wannan bincike, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya bayyana wa majalisar cewa yawancin cibiyoyin horas da jami’an tsaro na cikin mummunan hali matuƙa, yana mai jaddada cewa lamarin yana buƙatar a ɗauki matakin gaggawa saboda barazanar da ke tattare da shi ga tsaron ƙasa.

Bayan gabatar da rahoton, Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatin tarayya na tinkarar matsalar gaba ɗaya.

Haka kuma, ya yi kira ga gwamnonin jihohi 36 da su tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da suke aiwatarwa sun zama masu amfani kai tsaye ga rayuwar al’ummarsu.

Shettima ya jaddada cewa mulki ba shi da nasaba da takardu ko jawaban baki kaɗai, illa sakamako da jama’a za su gani su kuma ji a zahiri. Ya ce, dole ne a mayar da hankali kan aiwatar da manufofi maimakon yawan furuci.

By ukarofi