Kungiyar tsofaffin ɗalibai GWAMOBA ta yi taron cika shekaru 20 da kammala makaranta 

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Kungiyar tsofoffin ɗalibai ta GWAMOBA wato Gwammaja 2 Old Boys Association 2005 ƙarƙashin shugabancin Auwalu Haruna, da maitamakinsa Adamu Usman ta yi taron bikin cika shekaru a 20 wanda aka yi a gidan tunawa da marigayi da Malamn Aminu Kano da ke unguwar gwammaja Kano Nijeriya 

A jawabinsa mataimakin Shugaban ƙungiyar GWAMOBA Adamu Usman wanda ke tare da Sakataren ƙungiyar Buhari Aliyu Muhammad sun bayyana maƙasudin wannan taro shi ne sadar da zumunci da taimakon juna a tsakanin ɗaliban na GWAMOBA wanda hakan ya sa aka zaɓo wasu daga cikin ɗaliban da suka ba da gagarimar gudunmawa wajen cigaban ƙungiyar da ‘ya’yanta ya sa aka ba su takardun shaidar karramawa domin ƙarfafa gwiwarsu kuma ƙungiyar za ta cigaba yin aiki na tabbatar da zumuci da maimakon juna dama sauran al’umma.

A ƙarshe Alhaji Makihu Abdullahi na ɗaya daga cikin fitattun ɗalibai da suka to makarantar 2 kuma guda daga cikin waɗanda GWAMOBA ta bawa takardar shaidar karramawa a wannan taro a wannan rana wanda kuma ya yaba da godiya a madadin ɗaukaci waɗanda aka karrama a wannan rana yace za su cigaba dukkanin wani na cigaban ƙungiya ta GWAMOBA da taimakata mata dama sauran al’umma baki ɗaya inda kuma ya yi addu’ar samun ƙaruwar arziƙi a Kano dama Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi