Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge, Honorabul Salisu Masu ya bayyana cewa fahimatar da gwamnatin Kwankwasiyya ta yi tun daga kan Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf babu wani abu da waɗannan gwamnatoci suka fi bai wa muhimmanci a manufarsu ta ɗaya ta biyu ta uku fiye da ilimi domin duk al’ummar da samu ilimi to ta gama samun cigaba a rayuwar duniya da lahira matuƙar akwai ilimin zamani an kuma yi aiki da shi to an gama samun cigaba kamar yadda Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge Hon Salisu Masu ya bayyana.
Haka kuma ya ce kasancewarsa wanda ya karanci harkar malanta tunda daga matakin gaba da firamare har zuwa gaba da sakandire kuma babu wani aiki da ya ƙware fiye da malanta wato harkar koyarwa, wannan ce ta sa ya ga manufar jagora Kwankwaso da gwamnan Kano ta yi musu daidai akan harkar bunƙasa ilimi a wannan ƙaramar hukumar ta Fagge a matsayin koyi da gwamna Abba Kabir Yusuf.
Haka zalika ya ce gyaran makarantu da gina ajijuwa da firamare ne ga da ake ginawa a wannan ƙaramar hukumar ta Fagge da ma sauran ayyuka na cigaban Fagge wato goyon baya ne da gudunmawa da yake samu daga gwamna wanda ya kawo miliyoyin nairori sama da miliyan ɗari 2 ya ce gashi ka je ka yi aiki ciyar da al’ummar Fagge gaba ta kowanne fanni kan haka ne ya ce shidai agunsa gwamna Abba ya ba ƙananan hukumomi yancin gashin kansu imma wani bai gani ba to ita dai Fagge imma akwai wani abu da ya fi ‘yancin gashin kai to ni dai shugaban ƙaramar hukumar Fagge na samu daga gwamna Abba Kabir Yusuf.
Shi ma Dakta Ibrahim Sallau Sakataren ilimi na ƙaramar hukumar Fagge ya ce akwai buƙatar Shugabannin ƙananan hukumomi da sauransu shugabanni na Kano a matakin ƙananan hukumomi da ma Nijeriya baki ɗaya su zama masu kishin ilimi kamar na Hon Salisu Masu Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge musamman yadda ofishin ES da sauran Fagge ofisoshi Shugaban ke kula da su da kuma ba su haɗin akan dukka wani aiki na cigaban al’ummar Fagge Kano Nijeriya.
