Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar ‘Yan Kasuwar ƙaramar Hukumar Bichi ts ‘Bichi Traders Multi-purpose Cooperatiɓe Society Limited’ ta kai ziyarar ban girma da neman shawarwari ga manyan shugabanni da malamai a garin Bichi da nufin bunƙasar harkokin kasuwanci da inganta tattalin arzikin ƙaramar hukumar.
A sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce da fari ƙungiyar ta kai wa Farfesa Arma Ya’u Hamisu Bichi ziyara wanda shugaba ne kuma jagoran al’umma, inda ya yi addu’a da fatan alkhairi ga ƙungiyar tare da bayyana farin ciki da jin daɗinsa a kan haka.
Sannan, ya yi alƙawarin bada gudunmawa wajen kafa gidauniya domin tallafa wa ’yan kasuwar da suka rasa jari, tare da tabbatar da cigaba da tuntuɓa da bada shawara domin daidaita kasuwancin yankin daidai da zamani.
Kazalika, ƙungiyar ta kai ziyarar ban girma ga babban malami kuma dattijo, Malam Abdullahi ɗangwani, yayin da shi ma ya yi addu’a tare da yi wa ’yan ƙungiyar nasiha bisa abubuwa kamar haka; kiyaye riba mai yawa, ha’inci da kuma cin amana.
Ya kuma ƙarfafe su da cewa arziki yana cikin noma, kiwo, kasuwanci da kuma ilimi na addini da na zamani.
Haka kuma, ƙungiyar ta ziyarci tsohon shugaban Bankin bayar da Lamunin Gina Gidaje na ƙasa reshen Jihar Kano, wato Alhaji Abdulfata Baba Yaro, inda aka bayyana shi a matsayin mutum na farko da ya fara tallafa wa matasa wajen buɗe shaguna da taimaka wa ƙananan ’yan kasuwa a yankin.
Alhaji Baba Yaro, ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa ’yan kasuwar ta hanyar sauke kaya a farashi mai sauƙi da kuma bayar da rance domin ƙarfafa wa ƙananan ’yan kasuwa.
Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta taimakawa wajen kawo dukkan nau’in kayan harkokin kasuwanci daga kamfanoni daban-daban.
“Wani abu da zamu fito da shi na ‘yan kasuwa ne; wanda bashi ne da za a iya ba ‘yan kasuwa daga naira miliyan 1. Zuwa naira miliyan 3. Kuma wannan bashin da za a ba mutum zai iya biya a cikin shekaru 10 ba takura ba takurawa, ko su ma’aikata yanzu duk bashin da muke ba su, idan muka ba ka bashin naira mliyan 1. A cikin shekaru 5 za ka biya, a kowane wata abin da za ka biya N19,000 ne”, inji shi.
Alhaji Baba Yaro ya kuma bayyana cewa duk lokacin da gwamnatin tarayya ta fito da wani tsari, za a fara aiwatar da shi a kasuwar ta Karamar Hukumar Bichi.
Daga bisani kuma ya yi addu’a tare da fatan alkhairi ga ƙungiyar da ’yan kasuwa da dukkan al’ummar yankin baki ɗaya.
