Kamar yadda RFK ta ruwaito, wani kwala-kwale ɗauke da mutane 400 ya kama da wuta a Arewa Maso Yammacin Congo, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 50 yayin da ɗaruruwa suka ɓace kamar yadda majiyoyin daga yankin suka sanar a ranar Laraba.
An samu nasarar ceto gwammai a haɗarin da ya faru a kogin Congo da tsakar daren Talata, da dama daga cikinsu ɗauke da raunuka, kodayake hukumomi na ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓata haɗin gwiwa da ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross.
Kwamishinan koguna Competent Loyoko ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AP cewa kwala-kwalan ya kama da wuta ne a garin Mbandaka, kuma ya tashi ne daga tashar jiragen ruwa ta Matankumu domin nufar yankin Bolamba.
Aƙalla mutane 100 da aka samu nasarar cetowa ne aka tsugunar dasu a ƙauyen Mbandaka, yayin da waɗanda suka ji rauni aka garzaya dasu asibitoci.
Loyoko ya ce lamarin ya samo asali ne lokacin da wata mata ta fara girki a cikin kwala-kwalan, a cewarsa da dama daga cikin fasinjoji da suka haɗa da mata da ƙananan yara sun rasa rayukansu bayan da suka tsunduma domin ceton ransu amma hakan bai yiwu ba saboda ba su iya iyo ba.
