Da alama dai matakin da Aljeriya ta ɗauka na korar wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Faransa 12, ya yi nasarar cire ran samun daidaito tsakanin ƙasashen biyu da wasu ƙasashe ke ƙoƙarin daidaitawa.
Umurnin dai ya kasance martani ga tuhume-tuhume da aka shigar a ƙasar Faransa ranar Juma’a kan wani jami’in karamin ofishin jakadancin ƙasar Aljeriya, da ake zarginsa da wasu ‘yan ƙasar Aljeriya biyu da hannu a sace ‘yan adawa a yankin Paris shekara guda da ta gabata.
Algiers ya zargi hukuncin kama jami’in a matsayin “babban cin zarafi ne da ya take kariya da ke tattare da ayyukan diflomasiyya.
A cewar kamfanin dillancin labaran ƙasar Aljeriya APS: “Wannan al’amari na shari’a da ba a taba ganin irinsa ba… bai zo kwatsam ba. Manufarsa ita ce ta wargaza duk wani yunƙuri na sake ƙulla alaƙa tsakanin ƙasashen biyu da shugabannin ƙasashen biyu suka amince.”
Tattaunawar da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune a ƙarshen watan Maris wata alama ce ta farko ta yiwuwar yin sulhu bayan shafe watanni ana rikici.
Mako guda bayan wannan, Algiers ya karɓi baƙuncin Jean-Noël Barrot, ministan harkokin wajen Macron, wanda da alama ya tabbatar da aniyar ɓangarorin biyu na buɗe wani sabon shafi na alaƙa a tsakaninsu.
Sai dai wannan gagarumin hukuncin na korar mafi girma da aka yi wa ma’aikatan ofishin jakadancin Faransa tun bayan samun ‘yancin kai a Aljeriya a shekarar 1962 – na nuni da cewa, har yanzu muryoyin adawa da Faransa na ci gaba da ƙaruwa a cikin da’irar gwamnatin Algiers.
Idan aka yi la’akari da ababen da suka wakana, za a fahimci cewa, a bayyane yake cewa ainihin matsalar Aljeriya ba Macron ba ce, mamimakon haka, harin nasu na kallon wasu ne a cikin gwamnatinsa – musamman ministan harkokin cikin gida Bruno Retailleau.
Retailleau mai ra’ayin mazan jiya, da ke da ra’ayin tsayawa takarar shugaban ƙasar Faransa mai zuwa – ya yi ƙaurin suna wajen furta kalamai masu tsauri kan baƙin haure, doka da oda, da dangantaka da Aljeriya.
Algiers na zargin sa hannun Retailleau a kama jami’in ofishin jakadancin. A fakaice dai ana zargin ministan cikin gidan ƙasar ne da ƙoƙarin kawo cikas ga tsarin, da kuma wuce gona da iri ta hanyar tsallake umurnin Macron kan rikicin na dangantaka da ke tsakanin su.
Wannan ne ya sa da yawa daga cikin jami’ai 12 da aka ba da umarnin fitar da su daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta Faransa ne, don haka ma’aikatan Retailau ne.
Masu sharhi na Aljeriya a kai a kai suna kai hari ga Faransawa dangane da amfani da damar da take da ita a Paris ta hanyar da bata dace ba, da kuma ƙoƙarin lalata dangantaka.
Sai dai a baya-bayan nan sun ƙara buɗa wuta ga Macron, duk da cewa shi ne da kansa ya haddasa rikicin a watan Yulin da ya gabata ta hanyar ayyana wani muhimmin sauyi ga abokiyar hamayyar Aljeriya ta Morocco.
Tun daga wancan lokaci taɓarɓarewar dangantaka ta kasance mafi muni tun bayan samun ‘yancin kai na Aljeriya.
