
Daga BELLO A. BABAJI
An samu rahoton ɓarkewar cutar kwalera a Jihar Borno bayan ambaliya da ta ɗaiɗaita kusan mutane miliyan biyu.
Cutar ta saba ɓulla a jihar tun daga bayyanar ta’addancin ƙungiyar Boko Haram daga shekaru 15 da suka gabata wanda ya ɗaiɗaita dubunnan al’umma zuwa sansanonin gudun hijira inda akan samu gazawa wajen tsaftace wuraren yadda ya kamata da kuma matsalar rashin isasshen ruwan amfani na yau da kullum.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Baba Mallam Gana ya ce an samu mutum 17 ɗauke da cutar bayan gwaji da aka yi, sai dai ba a samu rahoton mutuwa ba.
Ya ce, sun samu rahoto 500 waɗanda galibi daga ƙananan hukumomi biyar suka fito.
Hakan na zuwa ne bayan aukuwar ambaliya a watan da ya gabata sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alau wanda ya lalata gidaje da asibitoci da sauran kadarorin gwamnati da na al’umma.
