Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana a Abuja ranar Juma’a cewa rushewar tafiyar Kwankwasiyya na nan tafe a Kano, domin zai yi wuya a ga wani yana sanye da jar hula nan ba da jimawa ba.
Barau ya yi wannan bayani a ofishinsa lokacin da ya karɓi ɗaruruwan mambobin jam’iyyar NNPP da suka koma jam’iyyar APC.
A cewarsa, yadda ‘yan NNPP, ciki har da shugabanninsu, ke tururuwar shigowa APC, shaida ce ga ƙaruwar farin jinin da APC ke samu a Jihar Kano duk da kasancewarta jam’iyyar adawa a jihar.
Ya ce, “Zan ci gaba da karɓar ‘yan NNPP da ke tururuwar komawa jam’iyyarmu. Siyasa dama lamari ne na mutane. Idan kana da jam’iyyar siyasa kuma babu mutane to akwai matsala.
“’Yan NNPP suna jan hankalinsu zuwa APC ne saboda irin ayyukan da muke yi a fannoni daban-daban na jiharmu da ƙasa baki ɗaya, ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu.
“A lokacin da aka kafa APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zagaya faɗin kasa yana jawo mutane zuwa jam’iyyar. Kuma wannan shine dalilin da yasa jam’iyyar ta zama sananniya a ƙasa. Zamu ci gaba da karɓar mambobin NNPP da sauran jam’iyyu duk da abin da wasu ke faɗa.
“Lokaci zai zo. Za ka rika neman wanda ke sanye da jar hula, alamar Kwankwasiyya, amma ba za ka ga kowa ba a Kano. Zamu kai wannan matsayin ba da jimawa ba.
