Daga WAKILINMU
Sakamakon tuɓe wa mahaifinta rawani a matsayin Wazirin Bauchi da Masarautar Bauchi ta yi, ya sa Kwamishinar Bunƙasa Ƙungiyoyi, Ƙananan da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, Sa’adatu Bello Kirifi, ta yi murabus daga muƙaminta.
Sa’adatu Bello Kirifi ta yi murabus ne ƙasa da awa 24 bayan tuɓe wa mahaifin nata, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, rawaminsa na Wazirin Bauchi tare da sallamar sa daga Majalisar Masarauar a ranar Talata.
A takardar ajiye aikin da ta aike wa Gwamna Bala Mohammed ranar Laraba, Honorabul Sa’adatu ta ce, “Ina miƙa takardata ta yin murabus daga Majalisar Zartarwa da kuma kujerar Kwamishinar Bunƙasa Ƙungiyoyi, Ƙanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, ba tare da ɓata lokaci ba.
“Ina godiya ga Gwamna da ya ba ni damar yi wa Jihar Bauchi aiki a gwamnatinka.”
