Daga WAKILINMU
Masarautar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Dokta Rilwanu Suleiman Adam ta tube wazirinta, Muhammadu Bello Kirfi, daga mukaminsa saboda rashin da’a ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.
Masarautar ta bayyana haka ne cikin wasiƙar da ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Janairu, 2023 da kuma sa hannun Sakataren masarautar, Shehu Mudi Muhammad.
Majiya ta kusa da Kirfi ta ce tuɓaɓɓen Wazirin ba ya ƙasar sakamakon ya yi tafiya balle kuma a ji ta bakinsa.
Ta ce idan Allah Ya yi dawowarsa, za su zauna su tattauna kan batun.
Idan dai za a iya tunawa, a 2017 Sarkin Bauchi ya dakatar da Kirfi wanda daga bisani Gwamna Mohammed ya dawo da shi a watan Agusta, 2022 .
Kirfi tsohon Minista ne a gwamnatin Shehu Shagari da ta Olusegun Obasanjo.
