Kwankwaso ya musanta ķin amincewa da tayin koma wa APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta rahoton da ya karaďe kafafen sadarwa da ke cewa ya caccaki APC tare da ķin amsa tayin Shugaba Bola Tinubu na ya koma jam’iyyar.

Labarin, wanda ya karaďe kafafen sada zumunta, ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya nemi Kwankwaso da ya dawo cikin APC amma ya ki amincewa, inda wai ya ce gwamma ya ajiye siyasa da ya koma jam’iyyar.

Haka kuma, a labarin, Kwankwaso ya ci alwashin kafa wata tafiya ta siyasa da za ta kawo ķarshen shugabancin APC a 2027.

Saida, a yayin tsokaci game da raďe-raďen ta shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya nesanta kansa da kalaman, inda ya bayyana su a matsayin karya da wasu masu kokarin karkatar da al’umma a siyasa suka kirkira.

Ya kuma ce, ya ďauki matakin yin shuru ne game da harkokin siyasa ne a yanzu bisa wasu dalilai, wanda kuma har zuwa wannan sauya bai sauya daga hakan ba.

Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya kuma kirayi al’umma da su riķa tantance labaran siyasa da aka jingina masa musamman waɗanda ake yaɗa su a Sohiyal Mediya da wasu kafafen labarai.

By Babaji