Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga NDC

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar NDC sakamakon sauya sunayen wasu ‘yan takarar da ɓangarensa ya gabatar a Kano.

Rahotanni sun nuna cewa shugabancin NDC a jihar ya maye gurbin wasu daga cikin ƴan takarar ne domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar rabon muƙamai da tikitin takara tsakanin ɓangaren Kwankwasiyya da tsoffin membobin jam’iyyar bisa tsarin kaso 60 da 40.

Shugaban NDC na Kano, Hussaini Isah Mairiga, ya ce matakin ya zama dole ne bayan an samu saɓani kan yadda aka aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tun farko, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

Wannan rikici na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya ayyana Kwankwaso a matsayin abokin takararsa na mataimakin shugaban ƙasa domin zaɓen 2027.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin rikicin na iya jefa sabon haɗin gwiwar adawa cikin ƙalubale yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027.

By Babaji