
Bayan kammala zaɓen shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid da aka gudanar a birnin Madrid na ƙasar Sifaniya a daren Litinin wayewar ranar, an tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar mai ci, Florentino Pérez ya sake lashe zaɓen.
Wannan nasara na nufin cewa Florentino Pérez zai ci gaba da riƙe muƙamin shugabancin Real Madrid na tsawon wasu ƙarin shekaru biyar masu zuwa, inda zai cigaba da jagorantar dukkan harkokin ƙungiyar a fannoni daban-daban na wasanni da gudanarwa.
A wannan zaɓe dai, Pérez ya fafata ne da ɗan takara mai adawa, Enrique Riquelme, inda aka bayyana cewa duk da nasarar Pérez, sakamakon ƙuri’un da Riquelme ya samu ya ba da mamaki sosai ga shugaban mai ci.
Rahotanni sun nuna cewa Florentino Pérez ya yi tsammanin zai samu nasara cikin tazara mai yawa, amma sakamakon ya nuna cewa gasar ta fi ƙarfi fiye da yadda aka zata.
A ƙarshe, an taya Florentino Pérez murna bisa wannan nasara, yayin da magoya baya da mambobin kulob ɗin ke ci gaba da bayyana fatan ganin ƙungiyar ta ci gaba da samun nasarori a karkashin jagorancinsa.
